Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Mutane da dama sun jikkata a arewacin Kivu bayan zanga-zangar adawa da MDD

Motocin dakarun MONUSCO a jamhuriyar Dimokradiyar Congo.
Motocin dakarun MONUSCO a jamhuriyar Dimokradiyar Congo. ALEXIS HUGUET / AFP

Kungiyar agaji ta Red Cross ta nuna damuwa kan yadda Asibitoci a lardin Kivu ta Arewa mai fama da rikici suka cika makel da mutanen da harbi ya jikkata bayan mummunar zanga-zangar adawa da kasancewar Majalisar Dinkin Duniya da ake ganin ta gaza wajen dakatar da kisan fararen hula a yankin na Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

Talla

Tun ranar biyar ga watan nan na Afrelu aka fara gudanar da zanga-zangar da yajin aiki a arewacin Kivi, domin nuna adawa da tawagar Majalisar Dinkin Duniya, sakamakon yadda kungiyoyin masu dauke da makamai ke cikin karensu babu babbaka wajen aikata kisan gilla, zanga-zangar da yayi sanadin mutuwar mutane 10.

Fiye da mutane 120 da suka ji rauni suna jinya a asibitoci a babban biranen Goma da Beni dake arewacin Kivu da taimakon kungiyar agaji ta Red Cross.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.