Chadi

Kotun Senegal ta ki amincewa da bukatar sakin Hissene

Tsohon Shugaban Chadi,Hissene Habre a kotu
Tsohon Shugaban Chadi,Hissene Habre a kotu AFP PHOTO / SEYLLOU

Hukumomin kasar Senegal sun ki amincewa da bukatar sakin tsohon shugaban kasar Chadi Hisene Habre da kotun Afirka ta yankewa hukuncin daurin rai da rai saboda cin zarafin Bil Adama a kasar sa.

Talla

Lauyoyin tsohon shugaban sun gabatar da bukatar ganin an sake shi a Babbar kotun Dakar ranar 29 ga watan Maris amma kotun taki.

Tun bayan kifar da gwamnatin shi a shekarar 1990, Habre ya samu mafaka a Senegal, kuma sakamakon matsin lambar kasashen duniya an kama shi a shekarar 2013 inda aka masa shari’a kan zargin cin zarafin Bil Adama da suka hada da kisa da kuma azabtar da mutane, abinda ya sa aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Tsohon Shugaban kasar chadi ,Hissene Habre
Tsohon Shugaban kasar chadi ,Hissene Habre FILES / AFP

Wata hukumar bincike da aka kafa a Chadi ta zargi Hissene Habre da cin zarafin mutane akalla 4,000 lokacin mulkin sa tsakanin shekarar 1982 zuwa 1990. Lauyoyin Habre sun bukaci sakin sa ne saboda halin lafiyar sa da kuma annobar korona wadda ke cigaba da yaduwa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.