Nijar

'Yan bindiga sun kashe fararen hula 19 a Jamhuriyar Nijar

Wasu daga cikin mazauna kan iyakokin Nijar,Burkina Faso da Mali
Wasu daga cikin mazauna kan iyakokin Nijar,Burkina Faso da Mali OLYMPIA DE MAISMONT AFP/File

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce akalla fararen hula 19 Yan bindiga suka kashe a kauyen Gaigorou dake Jihar Tillaberi kusa da iyakar Mali.

Talla

Hukumomin yankin sun ce sun kidaya gawarwakin mutane 19 daga cikin wadanda harin ay ritsa da su, yayin da wasu biyu suka jikkata daga harin da Yan bindigar suka kai akan Babura. Wani jami’in karamar hukuma a Dessa dake iko da Gaigorou yace Yan bindigar sun kai hari ne kan mutanen da suka je janaiza a makabarta, inda suka bude musu wuta, kafin daga bisani suka shiga kauyen suka dinga harbi kan mai uwa da wabi.

Wata mata tare da yaranta a kauyen Tamou dake wajen birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Wata mata tare da yaranta a kauyen Tamou dake wajen birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar. ASSOCIATED PRESS - TAGAZA DJIBO

Jami’in yace yau lahadi anyi jana’izar mutanen 19 da aka yiwa kisan gillar.

Yankin Tillaberi na fama da hare haren Yan bindigar dake alaka da kungiyar Al Qaeda saboda kusancin sa da iyakokin Mali da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.