Chadi-Ta'addanci

Mun murkushe daukacin 'yan tawaye-Sojin Chadi -Rahoto

Sojojin Chadi a fagen daga
Sojojin Chadi a fagen daga AFP - RENAUD MASBEYE BOYBEYE

Rundunar Sojin Chadi ta sanar da murkushe daukacin 'yan tawayen da suka kaddamar da hare-hare a lokacin gudanar da zaben shugabancin kasar.

Talla

Kakakin sojin Azem Bermendoa Agouna ya sanar da cewar, yanzu haka sojojin na ci gaba da farautar sauran burbushin 'yan tawayen da suka rage.

Shi ma Ministan Sadarwa kuma Kakakin Gwamnati Cherif Mahamat Zene ya sanar da cewar, an murkushe yunkurin 'yan tawayen da suka taso daga Libya.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya ce, an girke tankunan yaki guda 4 da tarin sojoji a hanyar shiga birnin N'Djamena da ke arewaci a yammacin Asabar, yayin da motocin soji ke ci gaba da fita suna tafiya inda ake fada da 'yan tawayen.

Ofishin Jakadancin Amurka ya bukaci ma’aikatansa wadanda aikinsu bai zama wajibi ba da su fice daga kasar saboda kauce wa hari, yayin da ita ma Birtaniya ta bukaci 'yan kasarta da su gaggauta barin Chadi.

Shugaban kasar Chadi
Shugaban kasar Chadi AFP - LUDOVIC MARIN

A makon jiya kungiyar 'yan tawayen ta FACT ta sanar da kama sansanin sojin da ke kusa da iyakar Nijar da Libya.

Wakilin mu Mustapha Tijjani Mahdi daga Chadi ya aiko da wannan rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.