Mali - Ta'addanci

Mutane 40 sun mutu sakamakon rikicin mafarauta da 'Yan bindiga a Mali

Yankin Mopti
Yankin Mopti REUTERS/Adama Diarra

Akalla Mutane 40 suka mutu sakamakon wani fada da aka gwabza tsakanin mayakan dake ikrarin jihadi da mafarautan gargajiya kamar yadda hukumomin Mopti dake tsakiyar Mali suka sanar, yayin da sama da mutane 1,000 suka rasa matsugunan su.

Talla

Hukumomin sun ce an fafata ne tsakanin bangarorin biyu mazauna garuruwan Mopti da Djenne kuma kowanne bangare yayi asarar akalla mutane 20, a daidai lokacin da hukumomin suka tura Karin sojoji domin tabbatar da zaman lafiya. Wani jami’in tsaro ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar an samu barkewar fadan ne lokacin da mafarautan suka nemi karbar shinkafar da masu ikrarin jihadin suka karbe a matsayin haraji daga wurin su.

Mafarauta yan kabilar Dozo na kasar Mali
Mafarauta yan kabilar Dozo na kasar Mali AP

Sidiki Diarra mai magana da yawun kungiyar mafarautan yace an fara tashin hankalin ne tun daga ranar 12 ga watan nan, kuma sun yi asarar ‘yayan su da dama, yayin da wasu kuma koma kauyukan dake makotaka da su.

Masu tsautsauran ra’ayi sun kaddamar da hare hare a arewacin Mali tun daga shekarar 2012 rikicin da ya yadu zuwa tsakiyar kasar da kuma kasashen Burkina Faso da Nijar dake makotaka da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.