Chadi-Deby

Makomar yaki da boko haram bayan rasuwar Idris Deby na Chadi

Dakarun Sojin Chadi a yakinsu da ayyukan ta'addancin Boko Haram.
Dakarun Sojin Chadi a yakinsu da ayyukan ta'addancin Boko Haram. AFP - RENAUD MASBEYE BOYBEYE

Babu yadda za a rubuta tarihin yaki da boko haram a yankin tafkin Chadi ba tare da sanya sunan shugaba Idris Deby na Chadi ba saboda gagarumar rawar da ya taka wajen bada sojoji da kuma gabatar da kan sa a fagen daga domin ganin an murkushe kungiyar. 

Talla

Wannan rikici na boko haram ya shafi kasashen da ke tafkin Chadi guda 4 da suka hada da Najeriya inda rikicin ya fara da Jamhuriyar Benin da Kamaru da kuma Chadi.

Wannan ya sa shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi suka amince da bukatar kafa rundunar hadin gwuiwa domin yaki da wannan kungiya ta boko haram, yayinda aka kafa cibiyar ta a birnin N’djamena.

Shekaru 12 bayan barkewar wannan rikici har yanzu ana cigaba da fafatawa tsakanin mayakan boko haram da ke dauke da makamai da kuma sojojin da suka fito daga wadannan kasashe guda 4.

Sau tari shugaba Idris Deby ya bayyana cikin kayan soji a fagen daga yana jagorancin dakarun sa wajen murkushe mayakan boko haram wadanda ke kai hare hare garuruwan da ke zagaye da Tafkin Chadi su na kashe mutane tare da jami’an tsaro.

Bayan wani kazamin harin da mayakn boko haram suka kai a watan Yulin bara inda suka kashe sojojin Chadi sama da 90, shugaba Idris Deby ya mayar da ofishin yankin Tafkin Chadi domin bai wa dakarun kasar kwarin gwiwar samun nasarar yakin wanda ya kai ga samun gagarumar nasara akan mayakan, abinda ya kai ga shugaban da kan sa ya yi shelar samun nasara da kuma karkade mayakan dake tsibirin kasar.

Wannan nasara ta sa Majalisar dokokin Chadi ta bashi mukamin Marshall, mukami mafi girma a kasar a wani kasaitaccen bikin da akayi a N’djamena.

Ganin irin gagarumar gudunmawar da shugaba Idris Deby ya bayar wajen yaki da boko haram, duk da matsalar ‘yan tawayen kasar sa da ake samu jifa jifa, yanzu haka wasu masu sharhi na bayyana fargaba dangane da makomar wannan rikici sakamakon rasuwar shugaba Idris Deby.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.