Chadi-Ta'addanci

Shugaban Chadi Idris Deby Itno ya rasu yana da shekaru 68

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno.
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno. MARCO LONGARI AFP/File

Shugaban Chadi Idris Deby Itno ya mutu yau talata yana da shekaru 68 a Duniya bayan samun raunuka a gwabzawar da ya jagoranci dakarunsu fatattakar ‘yan tawayen FACT a kasar mai fama da rikici.

Talla

Rasuwar Deby kamar yadda rundunar Sojin kasar ta bakin kakakinta Janar Azem Bemrandoua Agouna ta fitar, na zuwa ne sa’o’i kalilan bayan sanarwar nasararsa a zaben ranar 11 ga watan nan da gagarumin rinjaye.

Hukumar Zaben Chadi ta ce marigari shugaba Deby ya lashe kashi 79.32 na yawan kuri’un da aka kada.

Wata sanarwar Rundunar Sojin Chadin ta daban, ta ce dansa Deby Janar Mahammat Deby a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar Soji.

Chadi wadda ke matsayin kasa mafi karfi a yakin da ake yi da Boko Haram a yankin tafkin Chadi, mutuwar shugaban wanda ya shafe shekaru 31 yana mulkar kasar, ka iya zama babbar koma baya a kokarin kakkabe ta’addancin da ya addabi kasashen da ke makwabtaka da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.