Najeriya-Chadi
Mutuwar Deby ta sanya damuwa a zukatan al'ummar arewa maso gabashin Najeriya
Wallafawa ranar:
Shiyyoyin Najeriya musamman wadanda ke makwabtaka da kasar Chadi a yankin arewa maso gabashin kasar sun nuna matukar damuwa da makomar tsaro a yakin da ake da kungiyar boko haram bayan mutuwar shugaban Chadi Idriss Deby Itno a jiya Talata yayin karawarsa da 'yan tawayen FACT masu barazana ga tsaron kasar. Daga Maiduguri wakilinmu Bilyaminu Yusuf ya duba mana halin da ake ciki ga kuma rahotonsa.