Chadi-Deby

'Yan tawaye sun lashi takobin kai hari bayan mutuwar Deby

Kasashen duniya sun jinjina wa jarumtakar Deby wajen yaki da 'yan ta'adda.
Kasashen duniya sun jinjina wa jarumtakar Deby wajen yaki da 'yan ta'adda. AP - Jerome Delay

Kungiyar 'yan tawayen da ta kaddamar da hare-hare a kasar Chadi a makon jiya daga kasar Libya, ta yi alkawarin ci gaba da dannawa har cikin babban birnin N’djamena bayan rasuwar shugaba Idriss Deby Itno.

Talla

Kungiyar ta yi watsi da gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa wadda dan marigayi Deby wato Mahamat ke jagoran ta, tana mai cewa, za ta ci gaba da kaddamar da hare-hare a cikin kasar.

Kodayake Kakakin Kungiyar Kingabe Ogouzeimi ya ce, a halin yanzu sun jingine batun kaddamar da hare-haren har tsawon sa’o'i 15 zuwa 28 domin bai wa Mahamat Deby damar gudanar da  jana’izar mahaifinsa.

A ranar Juma'a mai zuwa ne ake sa ran gudanar da jana'izar marigayin.

Kasashen duniya musamman Faransa sun jinjina wa Deby bisa namijin kokarinsa wajen fatattakar mayakan Boko Haram da suka addabi zagayen Tafkin Chadi, yayin da suka bayyana shi a matsayin jarumi kuma gwarzon soja wanda ya mutu a fagen kare martabar kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.