ECOWAS

Barazanar tsaro: ECOWAS ta kaddamar da shirin shigar da mata tsarin zaman lafiya

Shugaban Ghana, kuma shugaban ECOWAS mai ci Nana Akufo Addo yayin taron kungiyar ECOWAS karo na 58 a Abuja, ta kafar bidiyo.
Shugaban Ghana, kuma shugaban ECOWAS mai ci Nana Akufo Addo yayin taron kungiyar ECOWAS karo na 58 a Abuja, ta kafar bidiyo. GhanaWeb

 Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta ya yamma, Ecowas ta kaddamar da wani sabon tsare-tsaren da zai taimaka wajen kare hakkokin mata da kuma shigar da su cikin tsarin kawo zaman lafiya a yankin.Ecowas ta ce barazanar tsaro a koda yaushe ya fi shafan matan, don haka dole a yi tafiya da su.Ga rahoton wakilinmu na Abuja, Mohammed Sani Abubakar.