Chadi - 'Yan Tawaye

'Yan Tawayen Chadi sun sanar da ci gaba da mutunta tsagaita wuta

Dakarun gwamnatin Chadi na sintiri kare birnin Djamena daga harin 'yan tawaye dake kokarin kifar da gwamnatin Deby, ranar Laraba 6 ga watan Fabrairun shekarar 2008.
Dakarun gwamnatin Chadi na sintiri kare birnin Djamena daga harin 'yan tawaye dake kokarin kifar da gwamnatin Deby, ranar Laraba 6 ga watan Fabrairun shekarar 2008. AP - Jerome Delay

‘Yan Tawayen Chadi da ake zargi da kashe shugaba Idris Deby Itno bayan da suka kaddamar da farmaki a yankin arawacin kasar, sun  bayyana cigaba da mutunta tsagaita wuta.

Talla

Shugaban kungiyar ta FACT Mahamat Mahdi Alli  da yanzu haka ke kasar Gabon yace a shirye suke su aiwatar da shirin duk da yake ko a jiya sai da sojojin Chadi suka ci gaba da kai musu harin sama  da bamabamai.

Yana mai gargadin cewa ya zama dole bangarorin biyu su kiyaye tsagaita wutar.

"Ba za mu iya mutunta yarjejeniyar sulhu ba tare da daya bangare ba. Dole ne a yi sulhu a bangarorin biyu. Ba za mu nade hannu kawai ana kashe mu ba.Inji shi.

A martanin da ya mayar, kakakin majalisar mulkin soji karkashin jagorancin dan Idriss Deby kuma magajinsa, Mahamat Idriss Deby, ya ce: suna cikin yanayi na yaki dole su ci gaba da ruwan bama-bamai kan ‘Yan tawaye.

"'Yan tawaye ne su, shi ya sa muke musu ruwan bama-bamai. Muna cikin yanayi na yaki, shi ke nan."

Faransa da kayenta na yankin Sahel sun halarci jana'izar Deby

A ranar Juma’ar da ta gabata, kasar Chadi ta gudanar da jana’izar ban girma ga Idriss Deby Itno, babban jigo a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya na yankin Sahel, kuma Faransa da kawayenta na yankin sun nuna goyon bayansu ga Mahamat Idriss Deby.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, a cikin girmamawarsa ga shugaban da ya mutu, ya ce: "Ka rayu a matsayin soja, ka mutu a matsayin soja, da makami a hannunka".

 Bazan amince a ci mutuncin Chadi ba

Macron ya ce "Faransa ba za ta taba barin kowa, ko a yau ko gobe, ya kalubalanci zaman lafiyar Chadi da mutuncin ta ba."

Amma Macron ya kuma yi kira ga sabuwar gwamnatin mulkin sojan da aka nada ta karfafa bukatar"kwanciyar hankali, tafiya tare da tattaunawa da kuma kafa gwamnatin dimokiradiyya" ta farar hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.