Chadi-Deby

Tsohon dan takarar shugabancin Chadi Albert Pahimi ya zama Firaminista

Albert Pahimi Padacké, dan takarar shugabancin Chadi da ya zo na biyu a zaben kasar na watan jiya kuma tsohon Firaministan Chadin.
Albert Pahimi Padacké, dan takarar shugabancin Chadi da ya zo na biyu a zaben kasar na watan jiya kuma tsohon Firaministan Chadin. AFP - DJIMET WICHE

Sabuwar Gwamnatin mulkin sojin Chadi ta nada tsohon Firaminista Albert Pahimi Padacke wanda ya zo na biyu a zaben da aka yi ranar 11 ga watan nan a matsayin sabon Firaministan kasar.

Talla

Sabuwar gwamnatin mulkin sojin kasar Chadi ta sanar da nadin Albert Pahimi Padacke a matsayin Firaminista kamar yadda dokar kasa ta bayyana domin jagorancin gwamnatin da za ta shirya zabe cikin watanni 18 masu zuwa.

Pahimi Padacke ne firaminista na karshe da ya yi aiki da shugaba Idris Deby Itno wanda mutuwar sa sakamakon ranukan da ya samu a filin daga ya bada damar kafa majalisar mulki ta soji wanda ke karkashin ‘dan sa Janar Mahamat Idris Deby mai shekaru 37.

Dokar da majalisar sojin ta gabatar ta ce Pahimi Padacke zai yi aiki tare da wasu ministocin gwamnatin rikon kwaryar da za a nada nan gaba.

Gwamnatin kasar a jiya lahadi ta sha alwashin murkushe shugaban kungiyar 'yan tawayen FACT Mahamat Mahadi Ali wanda ta zarga da laifuffukan yaki, inda ta bukaci taimakon gwamnatin Nijar wajen kamo shi da mayakan sa.

Kakakin gwamnatin Chadi Azem Bermandoa Agouna ya ce sun gano inda 'yan tawayen tare da shugabansu su ke taruwa a Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.