Somalia

'Yan adawar Somalia sun kwace iko da wasu sassan birnin Mogadishu

Wasu daga cikin mayakan 'yan adawar Somalia.
Wasu daga cikin mayakan 'yan adawar Somalia. REUTERS - FEISAL OMAR

Mayakan 'yan adawar Somalia sun mamaye wasu yankunan birnin Mogadishu kwana guda bayan wata fafatawar da suka yi tsakanin su da dakarun gwamnati sakamakon yunkurin shugaban kasar Mohammed Abdullahi Mohammed na tsawaita mulkin sa ba tare da bin ka’ida ba.

Talla

Mayakan sun sanya shinge wajen tattare hanyoyin mota a birnin, yayinda dakarun gwamnati suma suka ja daga da motocin su da kuma tankunan yaki a daya bangaren.

Wani shaidar gani da ido Abdullahi Mire ya ce bangarorin biyu sun ja daga ne a hanyoyin kasar suna jiran ko ta kwana.

Shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed da ake yiwa lakabi da Farmajo a farkon wannan wata ya sanya hannu akan wata doka da Majalisar wakilai ta amince da ita na karawa kan sa shekaru 2 bayan karewar wa’adin sa ba tare da amincewar majalisar dattawa ba.

Wannan ya harzuka 'yan adawa ciki har da wasu masu goya masa baya abinda ya kai ga fafatawa mai zafi da manyan makamai jiya lahadi a birnin Mogadishu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.