Chadi-Boko Haram

Boko Haram ta kashe sojojin Chadi

Shugaban rikon kwaryar Chadi, Janar Mahamat Kaka
Shugaban rikon kwaryar Chadi, Janar Mahamat Kaka Marco Longari AFP/Archivos

Mayakan Boko Haram sun kashe akalla sojojin Chadi 12 a wani kazamin harin da suka kai musu a yankin Tafkin Chadi, yayin da sojojin suka kashe maharan 40.

Talla

Gwamnan Yankin Mahamat Fadoul Mackaye ya sanar da kashe sojojin lokacin da mayakan suka kai musu hari a sansaninsu a ranar Talata.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan adawa ke gudanar da zanga-zangar adawa da Majalisar Mulki ta Soji da Mahamat Deby ke jagoranci.

Marigayi tsohon shugaban Chadi Idriss Deby Itno ya taka gagarumar rawa wajen murkushe mayakan Boko Haram a kasashen da ke zagayen yankin Tafkin Chadi, yayin da ya rasa ransa a yayin fafatawa da 'yan tawaye a fagen daga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.