Faransa-Chadi

Macron ya yi tir da afkawa masu zanga-zanga a Chadi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. © AP - Thibault Camus

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi wadai da tashin hankalin da aka samu yau a Chadi bayan matakin jami'an tsaron kasar na tarwatsa masu zanga zanga adawa da shugabancin Soji karkashin jagorancin dan Idris Deby wato Mahamat Deby.

Talla

Yayin da ya ke ganawa da shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU kuma shugaban Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Felix Tshisekedi a fadar sa, Macron ya ce su na bayyana damuwar su kan abinda ya faru wanda ya yi sanadiyar kashe wata mata guda a birnin N’Djamena.

Shugaba Macron ya bukaci majalisar mulki ta sojin kasar da ta mutunta alkawarin da ta yi na tafiya tare da kowanne bangare domin tabbatar da shirin zaman lafiya da kuma siyasa, inda ya ke cewa Faransa na adawa da duk wani yunkuri na bayyana wani a matsayin magajin Deby.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.