Chadi-Zanga-Zanga

Masu zanga-zangar adawa da Mahamat Deby sun kashe mace guda a Chadi

Shugaban Majalisar Soji ta Chadi Mahamat Idriss Deby Itno.
Shugaban Majalisar Soji ta Chadi Mahamat Idriss Deby Itno. © Tele Tchad via AP

Masu zanga zangar adawa da nadin Mahamat Deby a matsayin jagoran majalisar mulki ta soji a kasar Chadi yau sun kashe wata mata guda duk da haramta zanga zangar da sojoji suka bukaci ganin anyi.

Talla

Rahotanni daga birnin N’Djamena sun ce jami’an 'yan Sanda sun mamaye titunan birnin domin tarwatsa masu zanga zangar adawa da majalisar mulki ta sojin da ke karkashin Mahamat Deby wadda ta karbi mulki tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby Itno.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce mai gabatar da kara Youssouf Tom ya sanar da mutuwar wata mace guda lokacin da masu zanga zangar suka kai hari kan wata motar safa mai dauke da fasinja.

Tom ya ce sun kai harin ne a yankin Dembe da ke birnin, abinda ya sa sauran fasinjan da ke cikin motan suka gudu, amma ita matar taki gudu, dalilin da ya kai ga kisanta.

Wani mai gabatar da kara Ali Kolla Brahim ya tabbatar da mutuwar wani matashi a garin Mondou da ke da nisan kilomita 400 daga birnin N’Djamena.

'Yan adawa da kungiyoyin fararen hula suka kira zanga zangar saboda bayyana nada Mahamat Deby a  matsayin shugaban mulkin soji da suka bayyana a matsayin juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.