Chadi

Bangaren adawa a Chadi ya mikawa sabuwar gwamnati bukatunsa

Firaministan Chadi Albert Pahimi Padacké.
Firaministan Chadi Albert Pahimi Padacké. © AFP - Issouf Sanogo

Firaministan Chadi Albert Pahimi Padacke, zai kafa sabuwar majalisar ministoci a cikin mako daya mai zuwa, inda tuni ya fara ganawa da illahirin bangarorin siyasa da na fararen hula na kasar domin jin ra’ayoyinsu.

Talla

Firaminista Albert Pahimi Padacke wanda ya zo na biyu a zaben da aka yi ranar 11 ga watan nan shigarsa gwamnati ya biyo bayan bukatar kasashen Duniya ta shigar da fararen hula cikin jagorancin kasar na watanni 18 gabanin gudanar da zabe.

Pahimi Padacke da ke matsayin firaminista na karshe da ya yi aiki da marigayi shugaba Idris Deby, tun bayan nadinsa mukamin ya sha alwashin hada kan kasar da kuma shawo kan bangaren adawa da nufin sanin bukatunsu gabanin zaben kasar.

Feilx Nialbe jagoran ‘yan adawa a rusashiyar majalisar dokokin kasar, bayan ganawa da Firaministan ya bayyana bukatunsu gabanin mara baya ga gwamnatin kasar wanda ya kunshi mayar da Pahimi jagoran majalisar mulkin soji ta CMT.

Haka zalika dole sai an kafa sharadin Firaministan rikon kwarya da shugaban majalisar dokoki ta riko ba za su tsaya takara a zabuka masu zuwa ba.

Baya ga haka dole ne duk wani mataki da za a dauka ya kasance za a dauke shi ne bayan cimma jituwa a tsakanin bangarorin al’umma na kasar baki daya.

A cewar Nialbe akwai bukatar firaminista Pahimi ya gaggauta shirya taro domin sulhunta ‘yan kasa a cikin watanni uku masu zuwa, kuma duk wani mataki da wannan taro zai dauka, dole ne gwamnatin da ke kan karagar mulki ta aiwatar da shi.

Tsohon jagoran adawar a rusasshiyar majalisar Chadi ya kuma bayyanawa Firaministan cewa akwai bukatar gayyato ‘yan kasar da ke zaune a ketare, da wadanda ke dauke da makamai, da ‘yan adawa da kuma fararen hula domin ba da gudunmuwarsu ga ayyukan gwamnatin rikon kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.