Malawi-Hukuncin kisa

Kotu ta soke hukuncin kisa a Malawi

Shugaban Malawi, Peter Mutharika tsakiyar alkalai yana rantsuwar kama aiki ranar 28, mayun 2019
Shugaban Malawi, Peter Mutharika tsakiyar alkalai yana rantsuwar kama aiki ranar 28, mayun 2019 AMOS GUMULIRA / AFP

A yau Laraba kotun kolin Malawi ta haramta hukuncin kisa a kasar, kana ta yi umurnin a canza hukuncin  wadanda aka yanke wa masu  fuskantar kisa.

Talla

An dade da tanadar hukunci mai tsauri a kan wadanda aka samu da laifin kisan kai ko cin amanar kasa a Malawi, akwai kuma zabin aiwatar da irin wannan hukuncin a kan wadanda aka samu da aikata fyade.

Zalika, hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai na iya hawa kan wadanda aka samu da laifin fashi da makami da ya kai ga daukar rai ko haddasa mummunan rauni, ko kuma wadanda aka samu da laifin haura katanga ko fasa gidaje.

Sai dai babu wanda aka aiwatar da hukuncin kisa a kansa tun da zababben shugaban Malawi na farko Bakili Mulizi ya nuna rashin amincewarsa da hukuncin bayan da ya dare karagar mulki a shekarar 1994.

A wani hukunci mai mahimmanci da aka yanke a Larabar nan, alkalan kotun koli da suka saurari daukaka karar da wani wanda aka yanke wa hukuncin kisa ya shigar, sun ayyana hukuncin kisa a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki.

Har yanzu fiye da kasashe 30 a nahiyar Afrika ke da tanadi na hukuncin kisa a dokokinsu, amma kasa da rabinsu ne suka aiwatar da hukuncin a cikin ‘yan shekarun nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.