Burkina-Ta'addanci

Kotu ta wanke mutane 3 da ake zargi da harin ta'addanci a Burkina faso, I. Coast

Ta'adin da harin ta'addancin Burkina Faso ya yi.
Ta'adin da harin ta'addancin Burkina Faso ya yi. REUTERS/Joe Penney

Wata Kotu a Senegal ta wanke wasu 'yan kasar Mauritania guda 3 da aka tuhuma da laifin kai munanan hare haren ta’addanci har biyu a kasashen Burkina Faso da Cote d’Ivoire a shekarar 2016.

Talla

A wani abin da ake ganin kamar koma baya wajen yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Afirka ta Yamma, Kotun kuma ta daure wani dan kasar Faransa a kan zargin taimaka wa ayyukan ta’addanci.

Masu gabatar da kara sun zargi 'yan kasar Mauritanian guda 3 da ake tsare da su tun daga shekarar 2016 da mu’amala da wani dan kasar Mali Mimi Ould Baba Cheikh, daya daga cikin wadanda aka zarga da kitsa harin da aka kai kasashen biyu wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30, kuma rabin su 'yan kasashen waje ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.