Chadi-Ta'addanci

Chadi ta sanar da kisan daruruwan 'yan tawaye a yammacin kasar

Dakarun Sojin Chadi a fagen daga.
Dakarun Sojin Chadi a fagen daga. AFP PHOTO / STEPHANE YAS

Hukumomin Kasar Chadi sun yi shelar kashe daruruwan 'yan tawaye a fafatawar da suka yi da su a yammacin kasar wanda aka kwashe kwanaki 2 ana yi, yayinda suka ce sun yi asarar sojojinsu guda 6.

Talla

Mai Magana da yawun gwamnatin mulkin sojin kasar Janar Azem Bermandoa Agouna ya gabatar da sanarwar da ke cewa dakarun gwamnati sun yi nasarar murkushe kutsen da 'yan tawayen suka yi a Nokou da ke Arewacin Kanem jiya alhamis.

Janar Agouna ya ce sun yi nasarar kashe daruruwan 'yan Tawayen, kuma an kama 66 wadanda ake rike a matsayin firsinoni.

Dakarun Sojin na Chadi ko a 'yan kwanaki kalilan gabanin kisan tsohon shugaban kasar Idris Deby sai da suka hallaka 'yan tawayen fiye da 300 baya ga kame wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.