Noma-Afrika

Manyan hukumomin kudi za su hada hannu wajen yakar yunwa a Afrika

Wasu ma'aikatan sashen abinci a Afrika.
Wasu ma'aikatan sashen abinci a Afrika. ESSA AHMED AFP/File

Wasu hukumomin kudade na duniya sun yi alkawarin samar da Dala biliyan 17 domin zuba su a bangaren aikin noma da samar da abinci domin shawo kan matsalar barazanar yunwa a nahiyar Afrika baki daya.

Talla

Yayin gudanar da wani taro na musamman akan barazanar yunwar da aka yiwa taken ‘Ciyar da Afirka‘, Bankin Raya kasashen Afirka da Asusun Bunkasa Noma na Majalisar Dinkin Duniya da kuma taron Hukumomin Binciken ayyukan gona na Afirka sun yi alkawarin samar da wadannan makudan kudade domin zuba su cikin ayyukan da suka shafi noma a cikin shekaru 5 masu zuwa.

Sakamakon bayan taron da wadannan bangarori suka gudanar ya ce shugabannin kasashen Afirka 17 sun sanya hannu akan shirin bunkasa aikin noma wajen ribanya amfanin da ake samu ta hanyar samar da kayayyakin aikin noma na zamani da samar da kasuwa da kuma inganta bincike kan aikin noman.

Daga cikin kudaden da aka yi alkawarin samarwa, Bankin Raya Kasashen Afirka ya ce zai bada Dala biliyan 10 nan da shekaru 5 masu zuwa wajen taimakawa wadanna kasashe, yayinda wasu karin Dala biliyan 8 da miliyan 830 zai je ga harkokin kasuwacin amfanin gonar wadanda ake saran matasa su amfana da shi.

Hukumar samar da cigaba ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta bada Dala biliyan guda da rabi a cikin shirin wanda ake saran zai samar da ayyukan yi miliyan 10 nan da shekarar 2030.

Shi ma Bankin kasashen Larabawa ya yi alkawarin zuba Dala biliyan guda da rabi a cikin shirin, yayinda Bankin Islama ya ce zai zuba Dala biliyan 3 da rabi.

Gidauniyar Bill da Malinda Gates ta ce za ta samar da Dala miliyan 652 wadanda za a sanya cikin shirin nan da shekaru 3 masu zuwa.

Shi dai wannan shiri ana saran ya bunkasa manoma akalla miliyan 300 a fadin Afirka baki daya wadanda suka kunshi masu gonaki da kuma ‘yan kasuwar dake safara da kuma sayar da amfanin gonar a kasuwanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.