Kamaru-'Yan aware

'Yan awaren Kamaru sun kashe Sojin kasar 4 a wani farmaki

Hare haren 'yan aware na ci gaba da tsannata a yankunan da ke amfani da turancin Ingilishi na kasar ta Kamaru wanda ya tilastawa daruruwan iyalai barin matsugunansu.
Hare haren 'yan aware na ci gaba da tsannata a yankunan da ke amfani da turancin Ingilishi na kasar ta Kamaru wanda ya tilastawa daruruwan iyalai barin matsugunansu. © AFP

'Yan Awaren da ke yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi a Kamaru sun kashe sojojin kasar guda 4 sakamakon wani sabon farmaki da suka kai kan sansanin Sojin.

Talla

Gwamnan yankin Augustine Awa Fonka ya shaidawa gidan talabijin din gwamnati cewar 'yan awaren sun kai harin ne kan sansanin sojojin da ke Menfoung, abinda ya yi sanadiyar kashe hudu daga cikin su da kuma raunata guda.

Yankin Arewa maso yamma da kuma kudu maso yammacin Kamaru ya zama sansanin tashin hankali na sama da shekaru 4 da suka gabata, abinda ya sa Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji su ke zargin sojoji da 'yan awaren da cin zarafin fararen hula.

'Yan awaren sun fadada hare haren da su ke kai wa a yankunan zuwa kan sojoji da 'yan Sanda, abinda ya yi sanadiyar kashe mutane sama da 3,500 a yankin da kuma tilastawa sama da 700,000 barin gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.