Chadi

Gwamnatin sojin Chadi ta janye dokar hana fita da ta sa tun bayan mutuwar Deby

Shugaban gwamnatin sojin Chadi Mahamat Idriss Déby,
Shugaban gwamnatin sojin Chadi Mahamat Idriss Déby, AFP - CHRISTOPHE PETIT TESSON

Majalisar Mulkin sojin  kasar Chadi ta sanar da janye dokar hana fitar da ta saka kwanaki 12 da suka gabata, bayan sanar da rasuwar shugaba Idris Deby Itno.

Talla

Kakakin Majalisar sojin kasar Janar Azem Bermendoa Agunna ya sanar da cewar bayan Nazari a kan matakan da majalisar soji ta dauka a fadin kasar da kuma ingantuwar harkokin tsaro, gwamnati ta amince a janye dokar hana fitar da aka saka ranar 20 ga watan Afrilu.

Dokar hana fitar ta fara ne daga karfe 6 na yamma zuwa 5 na asuba, kafin daga bisani aka dage zuwa daga karfe 8 na yamma zuwa 5 na asuba.

Shugaba Idris Deby ya rasu ne sakamakon raunin da ya samu a filin daga lokacin fafatawa da 'yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.