Kenya-Covid-19

Korona ta kashe likitan nan mai kushe rigakafinta a Kenya

Wata mata kenan ke karbar allurar rigakafin Korona a Kenyan duk da kushe rigakafin da likita Karanja ya yi.
Wata mata kenan ke karbar allurar rigakafin Korona a Kenyan duk da kushe rigakafin da likita Karanja ya yi. AFP - YASUYOSHI CHIBA

Wani Likita da ya yi kaurin suna wajen yaki da maganin rigakafin cutar korona a kasar Kenya, Dr Stephen Karanja ya rasu sakamakon kamuwa da cutar makwanni bayan ya yi shelar cewar karbar allurar ba wajibi bane.

Talla

Dr Karanja wanda yake jagorancin kungiyar likitoci mabiya darikar Katolika ya bada shawarar amfani ne da maganin chloroquine da kuma shakar tiriri ya dade yana karo da Mujami’ar Katolika wadda ta goyi bayan maganin rigakafin.

Kungiyar Limaman darikar Katolika a Kenya ta nesanta kanta daga matsayin Dr Karanja dangane da sahihancin maganin rigakafin, inda ta bai wa jama’a shawarar karbar allurar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da gudanar da bincike kan maganin rigakafin da ake amfani da shi a Kenya da kuma tabbatar da sahihancin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI