Somalia-Farmajo

Shugaban Somalia ya bude hanyar gudanar da sabon zabe a kasar

Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed, na Somalia.
Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed, na Somalia. Yasuyoshi CHIBA AFP/File

Shugaban Kasar Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed ya kaddamar da wani taron tattaunawar jama’ar kasar da zummar ganin an gudanar da sabon zabe, abin da ya samu goyan bayan 'yan adawar.

Talla

Yayin jawabi ga Majalisar dokoki, shugaban ya yi watsi da shirin da Majalisar wakilai ta amince da shi a watan jiya wanda ya bashi damar ci gaba da zama a karagar mulki na Karin shekaru biyu ba tare da gudanar da zabe ba.

Abdullahi ya bukaci Firaministansa da ya jagoranci shirin gudanar da zaben kamar yadda 'yan adawa suka bukata domin kawo karshen tashin hankalin da ya biyo bayan shirin ci gaba da mulki ba tare da gudanar da zabe ba.

Kasashen duniya da dama sun gargadi shugaban da ya shirya zabe domin kawo karshen rikicin kasar ko kuma su sanya takunkumi a kasar da ke fama da rashin zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.