Chadi

An bukaci gwamnatin sojin Chadi ta sanya 'yan tawaye a tattaunawa

Shugaban mulkin sojin Chadi, Mahamat Deby.
Shugaban mulkin sojin Chadi, Mahamat Deby. Brahim ADJI Tchad Presidential Palace/AFP/File

Tsohon Shugaban kasar Chadi Goukoni Weddeye ya bukaci sabbin shugabannin mulkin sojin kasar da su saka 'yan tawaye cikin mutanen da za’a tattauna da su da zummar tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar.

Talla

Goukouni wanda ya jagoranci Chadi daga shekarar 1980 zuwa 1982 ya bukaci sasanta jama’ar kasar ta hanyar rungumar 'yan tawayen da suka fito daga kasar Libya.

Tsohon shugaban ya ce babu dalilin watsi da 'yan tawayen ta hanyar da zai dada lalata kasar, saboda haka ya dace a hau teburin tattaunawa da su.

Gwamnatin sojin Mali ta ce ba zata tattauna da 'yan tawayen ba wadanda ta bayyana a matsayin abokan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.