Cote d'Ivoire - Tattalin arziki

Rashin wutar lantarki na neman durkusar da arzikin Cote d'Ivoire

Titin De Gaule birnin Abidjan Côte d'Ivoire
Titin De Gaule birnin Abidjan Côte d'Ivoire © fr.zil/CC/Wikimedias Commons

Rashin wutar lantarki a Cote d’Ivoire ya fusata 'yan kasar da shugabannin ‘yan kasuwa, lura da irin illolin da rashin wutar ya haifar.

Talla

Masu amfani da wutan lantarki, da kungiyoyin kwadago da shugabannin 'yan kasuwa a kasar suna kira kan rashin wutar lantarki da ke addabar manyan biranen kasar, ciki har da babban birnin tattalin arziki Abidjan da ke da mazauna miliyan biyar a cikinsa.

Cote d’Ivoire ce ke samar wa kasashen da dama makamashi

Kasar da ke Yammacin Afirka na alfahari da bunkasar tattalin arzikinta cikin shekaru takwas da suka gabata kuma ta kasance jagorar yanki a fannin samar da makamashi.

A shekarar 2019 ta fitar da kaso 11 cikin 100 na lantarkinta mai karfin Megawatt 2,200 zuwa kasashen Ghana, Togo, Benin, Burkina Fasso, Mali da kuma Liberia, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna.

To sai dai a makon da ya gabata kasar ta gamu da cikas wajen wadata al’umma da wutan lantarki, lamarin da ya haifar da tabarbarewar tattalin arziki, wanda ma’aikatar makamashi ta dora laifin kan canjin yanayi da kuma karancin ruwa a madatsun ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI