Burkina-Ta'addanci

'Yan bindiga sun kashe fararen hula 30 a lardin Komandjari na Burkina Faso

Hare haren ta'addanci na ci gaba da tsananta a sassan Burkina Faso musamman lardin na Komandjari wanda ya tilastawa mutane da dama barin muhallansu.
Hare haren ta'addanci na ci gaba da tsananta a sassan Burkina Faso musamman lardin na Komandjari wanda ya tilastawa mutane da dama barin muhallansu. © AFP/Olympia de Maismont

Mutane akalla 30 ne suka rasa rayukansu, sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a wani kauye da ke gabashin kasar Burkina Faso a jiya litinin.

Talla

Lamarin dai ya faru ne a jiya litinin, inda ‘yan bindigar suka afka wa kauyen Kodyel da ke cikin lardin Komandjari tare da kashe fararen hula, kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito.

Bayanai sun ce maharan sun yi wa garin kawanya ne tun da sanyin safiya, inda suka rika bi gida-gida suna kashe jama’a, yayin da suka rika bi ta bayan wadanda ke kokarin tserewa suna bude masu wuta hatta a cikin jeji.

Wani jami’i a rundunar mayakan kare-kai da ke yankin da ake kira VDP ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce adadin wadanda aka kashen ya kai 30.

Shi dai kauyen Kodyel na cikin gundumar Foutouri ne a lardin Komandjari, wanda ya yi kaurin suna ta fannin yawan samun hare-haren ‘yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.