Mali - Faransa

An yi garkuwa da wani dan jaridar Faransa a Mali

Hoton dan jarida Olivier Dubois da aka haska a bangon shafinsa na Twitter
Hoton dan jarida Olivier Dubois da aka haska a bangon shafinsa na Twitter © Capture d'écran

An sake shiga Fargaba yau Laraba sakamakon sake garkuwa da ‘yan kasashen yamma a kasar Mali, bayan da wani dan jaridar Faransa ya bayyana cikin wani hoton bidiyo yana cewa wata kungiyar masu ikirarin jihadi da ke da alaka da Al-Qaeda tayi garkuwa da shi.

Talla

Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna Olivier Dubois, wanda ke aiki da kafofin yada labaran Faransa da dama, ba za a iya tantance shi kai tsaye ba, duk da cewa kungiyar kare ‘yancin ‘yan jaridu ta Duniya (RSF) da wani jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Faransa sun tabbatar da cewa ya bace.

Dan jaridar ya bukaci dauki

A cikin gajeren bidiyon mara kwanan wata mai tsawon dakika 20, Dubois, mai shekara 46, ya ce kungiyar da take kiran kanta na tallafawa Musulmai da Musulunci ta sace shi a ranar 8 ga watan Afrilu a yankin Gao dake tsakiyar kasar Mali, kungiyar ta’addanci mafi girma a yankin Sahel.

An ganshi zaune a kasa kan wata koren mayafi, cikin wani abu kamar tanti, yana sanye da riga ta gargajiya mai ruwan hoda, dauke da gemu.

Dan jaridar cikin kakkausar murya, ya roki ‘yan uwansa da dangi,  da abokai da kuma gwamnatin Faransa "da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kubutar da shi.

Tun 8 ga watan Afrilu aka sace shi

Baban sakataren kungiyar RSF Christophe Deloire, ya wallafa ta shafinsa na twitter cewar, "Olivier Dubois wanda ke aikin hada rahotanni a yankin Gao na Mali, tun a ranar 8 ga watan Afrilu ya bar otel dinsa kuma bai sake komawa ba.

"Wannan gogaggen dan jaridar, wanda galibi ke aiki da Le Point Afrique da Liberation, ya san wannan yankin mai matukar hadari sosai."

Deloire ya kara da cewa: "An sanar da mu kwanaki biyu bayan batansa. A yayin tuntubar editocin da ya saba yi wa aiki, mun yanke shawarar kada a bayyana wannan batu a bainar jama'a, don kar mu kawo cikas ga kokarin kubutar da shi"

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI