Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Sojoji zasu tafiyar da yankunan Jamhuriyar Demokradiya Congo 2 saboda tsaro

Sojojin Jamhuriyar Demokradiyar Congo a yankin Beni bayan harin 'yan ta'adda a shekarar 2020
Sojojin Jamhuriyar Demokradiyar Congo a yankin Beni bayan harin 'yan ta'adda a shekarar 2020 © AFP - ALEXIS HUGUET

Shugaban Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Felix Tshisekedi ya baiwa sojoji da 'Yan sanda karbe ikon kula da Yankunan Arewacin Kivu da kuma Ituri sakamakon kwarya-kwaryar dokar ta bacin da ya kafa.

Talla

Shugaban yace ya saurari koke koken mazauna wadannan yankuna dake fama da matsalar tsaro musamman mata da Yam mata, saboda haka ya kawar da shugabannin fararen hular dake aiki a yankunan inda ya maye gurbin su da sojoji da kuma 'Yan Sanda.

Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar Tharsice Kasongo Mwemba yace daga ranar 6 ga watan nan wadannan yankuna guda biyu zasu shiga cikin dokar ta bacin na kwanaki 30, kuma za’a tafiyar da yankunan ne a karkashin dokar soji.

Sojan Monusco a yankin Beni, dake Demokradiyar Congo a watan Nuwambar 2018
Sojan Monusco a yankin Beni, dake Demokradiyar Congo a watan Nuwambar 2018 AFP - JOHN WESSELS

Ayyana dokar kwarya-kwarya dokar ta baci

A farkon watan nan na Mayu Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ta ayyana kwarya-kwaryar dokar ta - baci a larduna 2 dake gabashin kasar  da kungiyoyi masu daukar makamai suka addabi al’umma.

Wani dan majalisar dokokin kasar, Patrick Muyaya  ya shaida wa manema labarai cewa shugaban  Felix Tshekidi ya bayyana wa majalisar  shawarsa ta ayyana wannan kwarya-kwaryar dokar-ta-baci duba da yadda matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a lardunan arewacin Kivu da Ituri.

Shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo Félix Tshisekedi, yayin wata ziyara Faransa ranar 27 ga watan Afrilu  2021
Shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo Félix Tshisekedi, yayin wata ziyara Faransa ranar 27 ga watan Afrilu 2021 © RFI/Pierre René-Worms

A karkashin dokokin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, shugaban kasa na iya ayyana dokar ta baci ko kwarya kwaryar ta idan yanayin da ake ciki na barazana da yancin kasar ko mutuncinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI