Mali

Wata 'Yar kasar Mali ta haifi jarirai 9 kuma suna cikin koshin lafiya

Wani Likita dake kula da jarirai da aka haifa a wani asibi dake Gauhati, na kasar India, 11 ga watan Yuni 2014.
Wani Likita dake kula da jarirai da aka haifa a wani asibi dake Gauhati, na kasar India, 11 ga watan Yuni 2014. © AP - Anupam Nath

Wata mata 'yar kasar Mali ta haifi jarirai 9 a wani asibitin kasar Marokko ranar Talata kuma dukkan su suna "cikin koshin lafiya", in ji gwamnatinta, duk da cewa har yanzu hukumomin Morocco ba su tabbatar da abin da zai kasance ba, a wannan lamari da bas a ban ba.

Talla

Sanarwar da gwamnatin Mali ta gabatar tace tun ranar 30 ga watan Maris aka dauki matar 'yar shekaru 25 mai suna Halima Cisse, daga arewacin kasar zuwa Morocco domin samun kyakkyawar kulawa, tun bayan da akayi hasashen tana dauke da ‘yan 7 a cikin ta.

Mata biyar da Maza hudu

Ministan lafiyar Mali Fanta Sibi cikin wata sanarwa tace Matar ta haifi ‘yan mata biyar da maza hudu, kuma uwar da yaran 9 na cikin koshin lafiya kuma nan bada dadewa za’a mayar da su gida.

Likitocin kasar sun damu matuka dangane da lafiyar Cisse, a cewar rahotanni na cikin gida, da kuma damar da jariran ke da shi na rayuwa.

Binciken farko ya nuna matar na dauke 'yan 7

Ma’aikatar lafiyar Mali ta fada a cikin wata sanarwa cewa, binciken da aka gudanar a fadin kasashen Mali da Morocco ya nuna cewa Cisse na dauke da jarirai bakwai sabanin 9 da ta haifa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI