Burkina-Ta'addanci

'Yan ta'adda sun kashe mutane 25 a Burkina Faso

Taswirar kasar Burkina Faso.
Taswirar kasar Burkina Faso. © RFI

Hukumomi a  Burkina Faso, sun tabatar da mutuwar mutane 25, bayan wani hari da masu ikrarin jihadi suka kai a wani kauye, a yayin da aka kashe mahara 11. Kasar Burkina faso tana fama da hare haren masu ikirarin jihadi tun shekara 2015.

Talla

Harin shine mafi muni a cikin shekaru biyar da kasar ta dauka tana yaki da masu ikrarin jihadi.

Cikin wadanda suka mutu, 11 Ma’aikatan sa-kai ne da ke taimaka wa jami’an tsaro samar da bayanai bayan samun horo

A kalla mutane 1.300, ne aka kashe sama da miliyan daya suka bar gidajensu tun lokacin da masu ikraren jahadi suka fara tada kayar baya a shekara ta 2015.

Ministan sadarwa kasar ya tabatar da cewa a yanzu haka hukumomi sun kadamar da wani hari na musaman domin fatattakar masu ikrarin jihadin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.