Chad - 'Yan tawaye

Ministan tsaron Chadi yayi ikirarin fatattakar 'yan tawaye

Sojojin kasar Chadi, yayin sintiri a sassan birnin N'Djamena.
Sojojin kasar Chadi, yayin sintiri a sassan birnin N'Djamena. AP - Jerome Delay

Sabon ministan tsaron Chadi Brahim Daoud Yaya ya ce ‘yan tawayen kasar da suka kaddamar da farmakin da yayi sanadin mutuwar tsohon shugaba Idris Deby sun tsere, yayin da dakarun kasar ke cigaba da farautar su.

Talla

Yayin taron menama labaran da ya jagoranta a ranar Alhamis, ministan tsaron na Chadi Brahim Yaya, ya ce tuni dakarun kasar suka kame mayakan ‘yan tawayen da dama a cigaba da kakkabe sassan yankin arewacin kasar da suka mamaye a baya, tare da jadadda matsayar ba za su tattauna da su ba.

Sabon ministan tsaron ya kara da cewar kawo yanzu mayakan ‘yan tawaye 246 suka kama tare da gurfanar da su gaban shari’a, yayin da dakarun Chadi ke cigaba da kokarin murkushe ragowar mayakan da suka ja tunga a garin Nokou dake yankin Kanem.

Ranar 11 ga watan Afrilun da ya gabata, ‘yan tawayen kungiyar FACT da babban sansaninsu ke Libya, suka kaddamar da farmaki kan dakarun Chadi a daidai lokacin da aka soma zaben shugaban kasa.

Bayan barkewar sabon fadan ne, tsohon shugaba Idris Deby ya jagoranci sojojin Chadi da zummar murkushe ‘yan tawayen, sai dai ranar 19 ga watan na Afrilu rundunar sojin kasar ta sanar da mutuwarsa sakamakon raunukan da ya samu yayin fafatawa da masu tayar da kayar bayan a yankin na Kanem dake gaf da iyakar Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.