Guinea - Muhalli

Kasa ta rubza kan mahakan Zinare da dama a arewacin Guinea

Wani wurin hakar ma'adanai a yankin arewa maso gabashin kasar Guinea.
Wani wurin hakar ma'adanai a yankin arewa maso gabashin kasar Guinea. © AP

Mutane akalla 15 ne suka rasa rayukansu a yankin Siguiri dake arewa maso gabashin kasar Guinea, sakamakon rubzawar da ramin hakar zinaren da suke ciki yayi.

Talla

Masu aikin ceto sun ce hatsarin ya auku ne a kauyen Tatakourou sakamakon fadawar da wani dutse yayi kan gefen ramin hakar ma’adanan, sai dai ba a tantance ko dutsen ne ya danne mutanen ba, ko kuma kasar da ta rubza ce ta kashe su.

Makamancin wannan hatsarin dai ya taba aukuwa a kasar Guinea cikin watan Fabarairun shekarar 2019, abinda yayi sanadin  mutuwar  mahakan zinare 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI