Burkina Faso - Cote D' Ivoire

Burkina da Cote d'Ivoire sun sha alwashin murkushe ta'addanci

Wani sojan kasar Burkina Faso yayin atasaye kan yaki da ta'addanci.
Wani sojan kasar Burkina Faso yayin atasaye kan yaki da ta'addanci. © REUTERS/LUCGNAGO

Ministocin Tsaro na kasar Burkina Faso da Cote d'Ivoire sun lashi takobin tabbatar da ganin cewar kasashensu su sun yi bankwana da annobar masu tsatstsaurar akida dake kaddamar da Jihadi da karfin tsiya da suka addabi kasashen nasu.

Talla

Hare-haren ta’addancin dake karuwa a baya bayan nan dai sun yi sanadiyar hasarar rayuka da dama gami da dimbin dukiya a kasashen Sahel da suka hada da su Mali, Nijar, Burkina Faso, yayin da matsalar ke neman bazuwa zuwa wasu tsirarun yankunan Ivory Coast.

A kasar Burkina Faso kawai mutane akalla dubu 1 da 300 aka kashe yayinda wasu fiye da miliyan daya suka tsere daga muhallansu.

A ranar Litinin 10 ga watan Mayun nan ministocin Burkina Faso da na Ivory Coast suka tattauna  a birnin Ouagadoudu game da yadda za su tunkari lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.