Jamhuriyar Congo

Ana zargin ma'aikatan agaji da cin zarafin mata fiye da 20 a Congo

Wata mata da ta warke daga cutar Ebola a gidanta dake garin Beni a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.
Wata mata da ta warke daga cutar Ebola a gidanta dake garin Beni a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo. © Getty

Masu bincike a Jamhuriyar Congo sun ce mata fiye da 20 sun gabatar da korafi kan ma’aikatan kungiyoyin agaji da dama, wadanda suka ce sun ci zarafinsu ta hanyar fyade ko yunkurin hakan, a gabashin kasar ta Congo.

Talla

Jami’ai sun ce adadin matan 22 da suka gabatar da korafin a garin Butembo, sun ce aa ma’aikatan agaji maza dake taimakawa wajen yaki da annobar Ebola sun sama musu guraben ayyuka amma bisa musayar yin lalata da su, a cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta The New Humanitarian da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

14 daga cikin matan sun ce ma’aikatan da suka ci zarafin nasu sun gabatar musu da shaidar zama ma’aikatan agaji a karkashin hukumar lafiya ta duniya WHO.

Binciken ya kuma gano cewar daya daga cikin matan da suka yi korafi har ta rasa ranta a yayin kokarin zubar da juna biyun da ta samu, domin boyewa mijinta da kuma yaranta abinda ke faruwa.

Garin Butembo dake zama cibiyar kasuwancin lardin arewacin Kivu, ya fuskanci munin annobar Ebola da ta kashe mutane akalla 2, da 200, bayan sake barkewar da ta yi a tsakanin 2018 zuwa 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI