Ivory Coast - Tattalin Arziki

‘Yan sandan Ivory Coast sun ceto yara 68 daga aikin bauta a gonakin Cocoa

Matsalar bautar da kananan yara a gonakin Cocoa na ciwa gwamnatin kasar Ivory Coast tuwo a kwarya.
Matsalar bautar da kananan yara a gonakin Cocoa na ciwa gwamnatin kasar Ivory Coast tuwo a kwarya. Benjamin Lowy

‘Yan Sandan Ivory Coast sun ceto kanan yara akalla 68 da ake bautar da su a wasu manyan gonakin noman Cocoa a garin Soubre dake yammacin birnin Abidjan.

Talla

Soubre na daga cikin yankuna masu arzikin Cocoa a Ivory Coast, inda a yanzu haka, gwamnati ke fafutukar yaki da bautar da yara kanana ko kuma tilasta musu aiki a gonakin noman albarkar gonar na Cocoa.

Bincike dai ya nuna cewar mafi akasarin kananan yaran da ake bautar da su wajen noman Cocoan a kasar ta Ivory baki ne daga makwafciyar ta Burkina Faso, wadanda ya kama ta a ce yanzu haka suna halartar makarantu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI