Mali - Ta'addanci

Majalisar Dinkin Duniya ta tir da datse hannuwa da 'yan ta'adda ke yi a Mali

Taswirara duniya da ke nuna Mali.
Taswirara duniya da ke nuna Mali. Google Maps

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali ta bayyana bacin ranta dangane da dadatse hannuwan da wasu mayaka  da ke ikararin jihadi suka aikata ga wasu mutane da su ka zarga da sata, al’amarin da ke tunatar da abin asshan da gungun mayakan  da ke  goyon bayan kungiyar Al’qaeda suka aikata a 2012 a kasar.

Talla

Mayakan da ke dauke da makamai sun taru ne a ranar 2 ga wannan wata na mayu da muke ciki, a wata kasuwa dake garin Tin Hama, kusa da Ansongo dake arewacin kasar ta Mali, inda suka gabatar da wasu mutane uku da suka datsewa hannuwan  dama da kafafun hagu, bayan da suka danganta su da zama  barayi,  wadanda kamar yadda shaidun da suka halarci lamarin da suka bukaci sakaya sunansu saboda dalilan tsaro suka sanar.

Mayakan dake ikararin jihadin da suka aikata ta’asar da sunan Musulunci 'yayan kungiyar  ISIS a yankin babbar Sahara  (EIGS) ne, daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke ikararin jihadi a yankin Sahel.

Rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali da ta yi tir  da lamarin, tare da yin tini da makamancin wannan abin asshar da ya wakana a 2012,  Inda gungun mayakan da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda suka shiga raba jama’a da suke zargi da sata ko kortanci  da gabban jikinsu, ko rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.