Jamhuriyar Congo

Shugaban Congo ya nemi agajin EU da Uganda don murkushe 'yan ta'adda

Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo Felix Tshisekedi
Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo Felix Tshisekedi AP - Jerome Delay

Sojojin kasashen Turai ka iya sake komawa Jamhuriyar Congo a karon farko cikin shekaru 14, biyo bayan shawarar da shugaba Felix Tshisekedi ya yanke ta gayyato dakarun Turan domin taimaka musu wajen yiwa ‘yan tawayen kasar kwaf daya.

Talla

A matakin farko dai, shugaba Tshisekedin ya soma tuntubar kungiyar tarayyayr Turai EU ne kan bukatar soma baiwa dakarun Jamhuriyar Congo horo, batun da ministan tsaron kasar ya tattauna da jakadan kungiyar ta EU a birnin Kinshasa tun ranar Talatar da ta gabata.

Baya ga kungiyar kasashen Turai, gwamnatin Congo ta kuma shiga tattaunawa da makwafciyarta Uganda domin kafa wata rundunar sojin hadin gwiwa da za ta murkushe mayakan ‘yan tawayen kungiyar ADF, da suka kuntatawa lardin arewacin Kivu.

Wasu sojojin Jamhuriyar Congo a lardin Arewacin Kivu.
Wasu sojojin Jamhuriyar Congo a lardin Arewacin Kivu. © Stringer / Reuters

Sabon yunkurin gwamnatin Jamhuriyar Congo na zuwa ne, bayan rahoton majalisar dinkin duniya da ya ce a shekarar bara kadai, mutane 851 mayakan kungiyar ADF suka kashe a lardin na  Arewacin Kivu.

Tun a farkon watan Mayun da muke, rundunar sojin Jamhuriyar Congo ta kaddamar da farmaki kan gwamman kungiyoyin ‘yan tawaye da na ta’addancin da suke rike da yankuna da dama a lardunan arewacin Kivu da kuma Ituri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI