Sudan - Faransa

Faransa za ta baiwa Sudan bashin dala biliyan 1.5

Fira Ministan Sudan Abdallah Hamdok tare da shugaban Faransa. Emmanuel Macron.
Fira Ministan Sudan Abdallah Hamdok tare da shugaban Faransa. Emmanuel Macron. REUTERS/Philippe Wojazer

Faransa ta ce za ta baiwa kasar Sudan rancen dala biliyan daya da rabi domin taimaka mata wajen biyan dimbin bashin da asusun bada lamuni na duniya IMF ke bin kasar.

Talla

Ministan Kudin Faransa Bruno Le Maire ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, yana mai cewa shugaban kasar Emmanuel Macron zai rattaba hannu kan takardar amincewa da bada bashin.

Le Maire yayi wannan bayani ne a wajen bikin bude babban taro kan taimakawa Sudan wajen kafa gwamnatin dimokradiyya a kasar.

Fira Ministan Sudan Abdallah Hamdok yanzu haka yana Faransa, inda yake burin Faransar za ta taimaka mata da bashin dala biliyan 60 don rage basukan da ake binta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI