AU-Nijar

Kungiyar AU za ta tallafawa yankin Sahel a yaki da ta'addanci

Shugaban gudanarwar kungiyar Tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat da shugaban kasar Nijar Bazoum Mohammed.
Shugaban gudanarwar kungiyar Tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat da shugaban kasar Nijar Bazoum Mohammed. © AP

Shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat ya gana da shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed a birnin Paris inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kungiyar G5 Sahel da ke yaki da 'yan ta’adda.

Talla

Mahamat ya ce ya gabatarwa shugaban Nijar halin da ake ciki a yankin Sahel da kuma kokarin da kungyar ke yi wajen ganin ta ceto yankin da ke fama da rikici da kuma bunkasa tattalin arzikin sa.

Shugaban na AU ya ce za su fara taron tattalin arziki wanda ya shafi kasashen da ke yankin G5 Sahel, inda ake saran bai wa kasashen da ke yankin kula ta musamman saboda yadda su ke kashe kashi daya bisa 3 na kasafin kudaden kasashen su wajen harkar tsaro.

Mahamat ya bayyana cewar ya nada Mammane Sidikou a matsayin Jakadan sa a Mali domin sanya ido kan halin da yankin ke ciki da kuma irin taimakon da ya dace a bai wa rundunar G5 Sahel da kasashen Sahel da kuma na Tafkin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI