Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo

Birnin Goma ya tsira daga aman wutar tsaunin Nyiragongo

Narkaken dutse gami da aman wutar da tsaunin Nyiragongo yayi a Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.
Narkaken dutse gami da aman wutar da tsaunin Nyiragongo yayi a Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo. REUTERS - STRINGER

Birnin Goma dake Jamhuriyar Congo ya tsallake rijiya da baya, bayan da narkeken dutsen da ya kwararo daga kan tsaunin Nyiragongo ya taya a wajen birnin.

Talla

Tuni dai hadin gwiwar jami’an ceto da hukumomin tsaron kasar ta Jamhuriyar Congo suka kwashe dubban mutane daga kauyukan dake zagaye da tsaunin na Nyiragongo, wanda aman wutar da kuma narkeken duten da yayi suka lakume dubban gidaje da daruruwan gonaki.

Yadda sararin samaniyar wajen birnin Goma ya turnuke sakamakon aman wutar da tsaunin Nyiragongo yayi. 22/5/2021.
Yadda sararin samaniyar wajen birnin Goma ya turnuke sakamakon aman wutar da tsaunin Nyiragongo yayi. 22/5/2021. REUTERS - STRINGER

Jami’an ceto sun ce mutane 5 suka rasa rayukansu sakamakon aman wutar tsaunin da aka fuskanta, lamarin da ya haifar da motsawar kasa har sau 12 da sanyin safiyar yau.

Kawo yanzu kididdiga ta nuna kimanin mutane dubu 7 suka tsere zuwa cikin kasar Rwanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI