Mali-Juyin Mulki

Juyin Mulki: Sojoji sun rushe gwamnatin rikon kwaryar Mali

tubabben shugaban wucin gadi na Mali Bah Ndaw da mataimakinsa Kanar Assimi Goita a Bamako, Mali.
tubabben shugaban wucin gadi na Mali Bah Ndaw da mataimakinsa Kanar Assimi Goita a Bamako, Mali. http://joko.hausa.rfi.fr/sites/hausa.filesrfi/imagecache/REUTERS

Mali ta shiga rudani bayan da jagoran sojin da suka yi juyin mulki a kasar a shekarar da ta gabata, Kanar Assimi Goita ya sanar da rushe gwamnatin rikon kwaryar kasar, biyo bayan wani garambawul da gwamnatin ta yi wa majalisar ministocin kasar dake yammacin Afrika.

Talla

Rikici na baya bayan nan da ya sake addabar kasar da mayaka masu ikirarin jihadi suke rike da dimbim yankunaya janyo caccaka daga kasashen duniya.

Hafsoshin sojin da suka fusata da garambawul da gwamnatin kasar ta yi wa majalisar ministocinta sun kama shugaba bah Ndaw da firaminista Moctar Ouane, suka kuma kai su sansanin sojin kati da ke wajen birnin Bamako, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito, kafin daga bisani a samu sanarwar tube su.

Mutanen biyu da aka kama dai su ke jagorantar gwamnatin rikon kwaryar da sojoji suka kafa don kauce wa barazanar takunkumai da kasashen duniya ke wa kasar, kuma yanzu kama su ya rikide zuwa wani juyin mulki, karo na biyu cikin shekara guda a kasar.

Wannan lamari ya auku ne bayan garambawul da suka wa gwamnatin kasar a ranar Litinin, garambawul da ya auku sakamakon sukar da ake wa gwamnatin rikon kwaryar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI