Faransa - Afrika

Macron ya goyi bayan samar da maganin cutar Korona a Afirka

Shugaban Afriika ta Kudu Cyril Ramaphosa tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birnin Pretoria. 28/5/2021.
Shugaban Afriika ta Kudu Cyril Ramaphosa tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birnin Pretoria. 28/5/2021. AFP - THEMBA HADEBE

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana aniyar sa ta goyan bayan sarrafa maganin cutar korona a nahiyar Afirka, nahiyar da har yanzu ba’a yiwa mutanen yankin allurar rigakafin ba.

Talla

Bayan tattaunawar da suka yi da shugaba Cyril Ramaphosa, shugaban Afirka ta Kudu, Macron yace yana da matukar muhimmanci a gare shi ya goyi bayan kasashe matalauta su samu maganin rigakafin.

Macron yace zasu zuba jari a cikin kamfanonin dake sarrafa magungunan a Afirka da zummar ganin an wadata yankin da shi.

Shugabannin biyu sun tattauna batun cire takunkumin samar da maganin a ko ina domin samar da yanayin da za’a wadata jama’a da shi.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yace babu yadda Afirka zata cigaba da dakon samun maganin rigakafin a daidai lokacin da jama’a ke cigaba da rasa rayukan su.

Kasar Afirka ta kudu ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka harbu da cutar, wadanda yawan su ya zarce miliyan guda rabi daga cikin mutane kusan miliyan 5 da suka harbu a Afirka, kuma ya zuwa yanzu kusan 130,000 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.