Mali-ECOWAS

ECOWAS ta dakatar da Mali saboda juyin mulkin Soji sau 2 a watanni 9

Shugaban gwamnatin Sojin Mali Kanal Assimi Goïta.
Shugaban gwamnatin Sojin Mali Kanal Assimi Goïta. REUTERS - FRANCIS KOKOROKO

Kungiyar ECOWAS ta sanar da dakatar da Mali daga jerin kasashe mambobinta yayin wani taro da shugabannin kasashen kungiyar suka gudanar jiya a Ghana, biyo bayan juyin mulkin Soji da kasar ta gani har sau 2 cikin watanni 9.

Talla

Matakin dakatar da Mali daga jerin kasashen na EOWAS ya diga ayar tambaya kan makomar tsaron al’ummarta sakamakon yadda hare-haren ta’addanci daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi da kuma rikicin kabilanci ke ci gaba da ta’azzara a sassan kasar ta yankin Sahel.

Taron wanda ya gudana jiya Lahadi bisa jagoranci shugabannin kasashe 10 da ministocin waje 2 a birnin Accra na Ghana kacokan ya mayar da hankali kan halin da Mali ke ciki.

Ministan harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor ya ce dakatarwar da aka yiwa Mali daga jerin kasashen na ECOWAS ya fara aiki ne nan ta ke daga jiya Lahadi 30 ga watan Mayu har zuwa watan Fabarairun 2022 lokacin da aka tsara Sojin za su mika mulki ga zababben shugaban farar hula.

Taron na ECOWAS wanda ya samu halartar masu shiga tsakani a rikicin siyasar Malin karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya karkare da bukatar ganin lallai kasar ta tabbatar da nadin farar hula a matsayin jagoran gwamnati.

Haka zalika sanarwar da ECOWAS ta fitar bayan taron ta nuna cewa babu ta yadda za a yi, shugaban gwamnatin Sojin kasar da mataimakinsa da ma Firaministansa su iya samun damar tsayawa takara a zaben da aka tsara gudanarwa a kasar don mika mulki ga fararen hula karkashin demokradiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI