Tigray-MDD

Kashi 90 na al'ummar Tigray a Habasha na bukatar agajin abinci- MDD

Wasu al'ummar yankin Tigray na Habasha.
Wasu al'ummar yankin Tigray na Habasha. © RFI/ Sébastien Németh

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla kashi 90 na mutanen yankin Tigray da ke kasar Habasha na bukatar agajin abinci, abin da ya sa ta kaddamar da gidauniyar dala miliyan 200 domin kai musu dauki.

Talla

Hukumar samar da abinci ta majalisar ta ce tashin hankalin da aka samu a yankin ya yi sanadiyar haifar da yunwa, abinda ke nuna cewar yanzu haka mutane miliyan 5 da dubu 200 ke bukatar agajin gaggawa, wanda ke nuna cewar shi ne kashi 91 na mutanen yankin.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya ne ya tura sojoji domin murkushe 'yan tawayen yankin da kuma kwace makaman su.

Ahmed ya ce matakin ya biyo bayan hare haren da 'yan tawayen TPLF suka kaddamar akan barikin sojojin dake yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.