Amurka tayi tayin bada ladar Dala miliyan 7 akan shugaban Al Qaeda

Sakataren harkokin wajen Amurka  Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken Ben STANSALL POOL/AFP/File

Kasar Amurka tayi tayin bada ladar Dala miliyan 7 ga duk wanda ya tsegunta mata inda zata sami shugaban kungiyar Al Qaeda dake Yankin Arewacin Afirka da ake kira Abu Ubaydah Yusuf al-Anabi.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen kasar tace an nada Anabi a matsayin shugaban Al Qaeda a Yankin Arewacin Afirka ne a watan Nuwambar shekarar 2020 bayan kashe wanda yake rike da mukamin Abdelmalik Droukdel watanni 5 kafin lokacin.

Sanarwar tace Anabi dan assalin kasar Algeriya ne kuma ana kiran shi da Yazid Mubarak, yayin da ya bayyana mubayi’ar sa ga shugaban kungiyar Al Qaeda ta duniya Ayman al Zawahiri.

Amurka tace Anabi na cikin Majalisar shugabannin kungiyar Al Qaeda ta Shura kuma ya taba zama shugaban bangaren sadarwar ta.

A shekarar 2015 Amurka ta sanya sunan sa cikin kundin Yan ta’adda na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.