Mali-AU

Kungiyar AU ta bi sahun ECOWAS wajen dakatar da Mali saboda juyin mulki

Jagoran mulkin Soji a Mali Kanal Assimi Goïta.
Jagoran mulkin Soji a Mali Kanal Assimi Goïta. MICHELE CATTANI AFP/Archivos

Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta sanar da dakatar da kasar Mali daga zama mambarta cikin gaggawa sakamakon juyin mulki Sojoji karo na biyu da kasar ta gani a cikin watanni 9.

Talla

Kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar ya sanar da daukar matakin wanda yace ya kunshi duk wasu harkokin da suka shafi kungiyar har sai zuwa lokacin da aka kafa gwamnatin farar hula.

Wannan mataki na zuwa ne bayan kungiyar ECOWAS ta dauki irin wannan mataki sakamakon taron shugabannin ta da ya gudana a kasar Ghana wanda ya samu halartar shugaban soji Assimi Goita.

ECOWAS ta bukaci Mali ta gaggauta nada Firaminista farar hula da kuma tabbatar da gudanar da zabe a watan Fabarairun shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.