Chadi-Afrika ta tsakiya

Ministocin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun isa Chadi bayan rikicin Soji

Wasu dakarun Sojin Chadi.
Wasu dakarun Sojin Chadi. - AFP/File

Ministocin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya guda 3 sun tafi kasar Chadi domin kwantar da hankalin gwamnatin kasar bayan kashe sojojin su guda 6 da dakarun Afirka ta tsakiyar suka yi akan iyaka.

Talla

Kakakin Gwamnatin Chadi Abderahman Koulamallah ya ce 5 daga cikin sojojin guda 6 da aka kashe, an harbe su ne bayan kama su da akayi, inda at bayyana matakin a matsayin wand aba zata amince da shi ba.

Kakakin gwamnatin Afirka ta Tsakiya Albert Yaloke Mokpeme ya ce ministocin 3 na dauke da wasika daga shugaba Faustin Archange Toudera, kuma za su gana da shugaban kasa Mahamat Idriss Deby domin bayyana bakin cikin su da abinda ya faru wanda suka danganta shi da yaki da 'yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.