Afrika na fuskantar dawowar korona zagaye na 3 - WHO

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus Christopher Black World Health Organization/AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya tace nahiyar Afirka bata yi wani shiri na tinkarar annobar korona karo na 3 dake zuwa ba ba tare da wata makawa ba sakamakon karuwar masu harbuwa da cutar da kuma karancin samun maganin rigakafin ta.

Talla

Daraktar Hukumar dake kula da nahiyar Afirka Dr Matshidiso Moeti tace asibitocin dake Afirka da dama da cibiyoyin kula da lafiya basu da kayan aikin da suka dace wadanda za'a karbi wadanda cutar ta yiwa illa domin kula da lafiyar su.

Matshidiso tace babu tantama cutar na shirin sake dawowa a karo na 3 a nahiyar sakamakon samun karuwar masu harbuwa da ita.

Hukumar Lafiyar tace ya zuwa wannan lokaci an samu mutane miliyan 4 da dubu 800 da suka harbu da cutar a kasashen Afirka baki daya, wanda shine kashi 2.9 na yawan mutanen da suka kamu da ita a duniya baki daya, yayin da kuma dubu 130 daga cikin su suka mutu, wanda shine kashi 3.7 na yawan mutanen da suka mutu a fadin duniya.

Daga cikin kasashe 23 da akayi nazari akan su a Afirka, akasarin su suna da gadon asibiti guda ne kacal a cibiyoyin kwantar da wadanda rashin lafiyar su tayi tsanani domin kula da mutane 100,000 kuma kashi guda bisa 3 ne kawai ke da na’urar taimakawa marasa lafiya yin numfashi da ake kira Ventilator.

Wurin tantance jama'a Kampala kafin su shiga Masallachi
Wurin tantance jama'a Kampala kafin su shiga Masallachi © SUMY SADURNI/AFP

Kasar Afirka ta Kudu ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka harbu da cutar a Afirka da yawan su ya kai miliyan guda da dubu 600, kuma dubu 56 da dari 439 daga cikin su sun mutu.

Hukumar Lafiya tace ya zuwa wannan lokaci kashi 2 na mazauna Afirka ne kawai suka karbi allurar rigakafin cutar, yayin da aka yiwa kashi 24 na mutanen duniya rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI